logo

HAUSA

Xi ya mika gaisuwar ban girma ga dattawa a jajibirin ranar tsofaffin kasar Sin

2024-10-10 13:56:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika gaisuwar ban girma ga dattawa a jajibirin Ranar Tsofaffin Kasar, wadda a bana ta fado ranar Juma’a.

Xi ya bayyana fatan cewa, dattawa za su samu kulawa mai kyau, su ji dadin rayuwarsu, su kuma ci gaba da cika burikansu.

Xi ya bayyana hakan ne a cikin wasikar da ya aike wa wakilan tsofaffi  na cikin shirin sa kai na kasar. (Mohammed Yahaya)