logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 339 a Nijar

2024-10-10 10:47:40 CMG Hausa

Bayanin da hukumar kare jama’a ta kasar Nijar ta fidda ya nuna cewa, ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba, ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 339 a kasar Nijar, yayin da mutane 383 suka jikkata, kana, kimanin mutane miliyan 1 da dubu 176 da dari 5 sun gamu da asara sakamakon bala’un da ruwan sama kamar da bakin kwarya suka haddasa.

Tun daga watan Yuni na bana, aka fara yin ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan kasar Nijar, a wasu wurare kuma, yawan ruwan sama ya karu da kaso 200 bisa dari idan aka kwatanta da na bara, lamarin da ya haddasa bala’u da dama kamar ambaliyar ruwa da sauransu, wadanda suka haddasa asarar rayuwa da dukiyoyi da dama, ana kuma gamuwa da matsalar karancin kayayyaki da dai makamantansu. (Mai Fassara: Maryam Yang)