Ana ci gaba da fafatawa a gasar La Liga ta Sifaniya
2024-10-10 15:16:10 CRI
Gasar cin kofin kwallon kafa ta zakarun kulaflikan Sifaniya wato La Liga ta shiga hutun kaka karo na 2, inda kungiyar Barcelona ke saman teburin gasar da maki 3 sama da Real Madrid, kuma ga sakamakon wasannin makon jiya da wasu kulaflikan suka samu.
1. Barcelona da dan wasan ta Lewandowski sun haskaka sosai
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi nasara kan Deportivo Alavés da ci 3 da nema, inda yayin wasan su da ya gabata, Robert Lewandowski ya ciwa Barcelona kwallaye 3, tun kafin tafiya hutun rabin lokaci, kuma hakan ya ba shi damar kara yawan kwallayensa a kakar bana zuwa 10.
Lewandowski ya yi amfani da damar kwallayen da Raphinha, da ta Eric Garcia suka mika masa, inda ya jefa su a ragar Deportivo Alavés, kungiyar da masharhanta da dama ke ganin da ma ba sa’ar Barcelona ba ce.
Kocin Barca Hansi Flick, ya fuskanci rashin nasara a wasan baya sakamakon yawan sauyin ‘yan wasa, amma a wasa da Deportivo Alavés ya gyara kuskurensa, inda ya shiga wasan da tawaga mai karfin gaske, lamarin da zai faranta ransa, ganin yadda kungiyar da yake horaswa ta buga wasanni 7 masu kyau cikin kasa da makwanni 4.
2. Raunin Carvajal na iya haifarwa Real Madrid matsala
Duk da nasarar da Real Madrid ta samu a gida, a wasan da ta doke Valladolid da ci 2 da nema, a daya bangaren ta gamu da matsalar raunin da dan wasan ta muhimmi, wato Dani Carvajal ya ji a wasan.
Carvajal mai shekaru 32 a duniya ya ji rauni a gwiwa, inda likitoci suka ce sai an yi masa tiyata, wadda za ta hana shi buga sauran wasannin kakar bana, kuma sakamakon haka, Madrid din za ta ci gaba da wasa ne tare da Lucas Vazquez a bangaren tsaron baya ta dama. Wasu masu fashin baki na cewa ko da Madrid din ta mayar da Vazquez dan wasan tsaron baya, ba lallai ne “kwalliya ta biya kudin sabulu ba”, musamman a gabar da Nacho Ferandez ya bar kungiyar zuwa kungiyar Al-Qadsiah ta Saudiyya, wanda hakan zai bar koci Carlo Ancelotti da kokarin cike gibi mai wuyar sha’ani yayin da ake tsaka da buga tarin wasanni.
Hakan na nufin dole Ancelotti ya nemo tawaga ta biyu don maye gurbin wasu daga ‘yan wasan da yake bukata, musamman ganin cewa kungiyar na da damar nemo dan wasan da zai maye gurnin Carvajal a watan Janairu.
3. Tsohon tsarin Atletico na iya haifar wa kungiyar da kalubale
Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta riga ta yi kasa a teburin La Liga da maki 7 kasan Barcelona, kana da maki 4 kasan Real Madrid, bayan da ta buga kunnen doki 1 da 1 da Real Sociedad a wasan karshen mako.
Yayin wasan na ranar Lahadi, dan wasan Atletico Madrid Antoine Griezmann, ya sanyawa abokin wasansa Julian Alvarez kwallon da ya jefa a raga tun a mintunan farkon wasan, amma maimakon su kara azamar kare wannan kwallo, sai suka yi sakaci har ‘yan wasan Real Sociedad karkashin kocin su Diego Simeone suka rama kwallon, aka kuma tashi kunnen doki 1 da 1.
‘Yan wasan Atletico sun yi kokarin saka kwallo a raga ne sau 4 kacal har karshen wasan, sai kuma kwallon da Alvarez ya ci. Wanda hakan ya baiwa abokan hamayyar su damar yi musu matsin lamba, har ta kai a mintuna 84 da take wasa Luka Sucic ya farke kwallon da Atletico ta jefa musu a raga.
A halin yanzu, kungiyar Atletico na kan gaba wajen kashe kudaden sayen ‘yan wasa, cikin jerin kungiyoyin kwallon kafar Sifaniya, amma duk da haka, sun gaza nuna wani kwazo da zai nuna za su iya lashe kofin na La Liga.
4. Kungiyoyi da dama na cikin matsi a gasar La Liga
Bayan wasannin karshen makon jiya, kungiyoyin kwallon kafa na Valencia, da Leganes, da Las Palmas, da Valladolid sun ci gaba da fafutikar kaucewa fadawa kasan tekur, inda ake ganin kungiyoyin Valencia da Leganes a kan gaba a wannan yanayi.
Las Palmas ta buga wasa da Celta Vigo, kuma duk da cewa Celta din ta kai mintuna 30 na karshen wasan da ‘yan wasa 9 ne kacal, Palmas ba ta yi nasarar rama kwallon da Borja Iglesias ya zura mata a raga ba. A wasan Valladolid da Rayo Vallecano kuwa sun tashi ne 2 da 1, Valladolid na da 1 Rayo Vallecano na da 2.
Masu fashin baki na ganin a wannan gaba da aka shiga hutun wasanni, mai yiwuwa a ga wasu sauye sauye a tsarin kulaflikan dake buga gasar ta La Liga, ciki har da wata kila mai horas da ‘yan wasa daya, da ka iya rasa aikinsa nan da ‘yan kwanaki, sakamakon gazawa a wasannin da aka riga aka buga.