UNDP tare da hadin gwiwa da gwamnatin jihar Katsina sun kaddamar da aikin gina gidaje 152 ga ’yan gudun hijra
2024-10-09 09:14:23 CMG Hausa
Gwamnatin jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda ya jagoranci bikin kaddamar da aikin gina gidaje 152 ga mutanen da hare-haren ’yan ta’adda a jihar ya yi sanadin kauracewa muhallansu.
A yayin bikin da aka gudanar jiya Talata 8 ga wata a karamar hukumar Jibia, gwamnan ya ce, aikin ginin gidajen aiki ne na hadin gwiwa da hukumar raya kasashe na majalissar dinkin duniya, inda kuma ya kara jaddada cewa, ba da dadewa ba matsalolin hare-haren ’yan ta’adda a jihar zai zamo tarihi.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Dr. Umar Dikko Radda ya yi bayanin cewa, shirin samar da gidajen yana daya daga cikin matakan da gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da kungiyoyin kasa da kasa ke bi domin dai saukaka yanayin rayuwar ’yan gudun hijirar dake jihar ta hanyar samar musu da matsuguni da kuma damarmakin ayyukan dogaro da kai.
Gwamnan ya ce, adadin iyalai dubu 2 ne dai za su amfana da wadannan gidaje wadanda suka fito daga kananan hukumomi 8 na jihar da hare-haren ta’addancin ya fi shafa.
“Wannan matsala ta tsaro shi ne dalilin da ya sa aka kalli cewa kafin a fara yin wani abu, abin da ya kamata a fara yin a gwamnatance shi ne a kalli mutanen da suka rabu da gidajensu, suka rasa dukiyoyinsu, suka rasa rayuwar masoyansu domin a ba su wuraren da za su tsuguna su da iyalinsu kuma a ba su kudaden da za su yi sana’o’i wanda za su rike rayuwarsu da ta ’ya’yansu da marayun da aka bar musu.”
A jawabinsa babban jami’in hukumar ta UNDP mai lura da shiyyar arewa maso yammacin Najeriya Mr. Ashraf Usman ya ce, shirin hadin gwiwar bai tsaya kawai ga gina gidaje ba, ya hada da aikin ganon ainihin kalubalen dake addabar yankin da nufin maganinsu gaba daya. (Garba Abdullahi Bagwai)