logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a mara baya ga kasashen yankin manyan tafkunan Afirka don karfafa hadin gwiwa

2024-10-09 09:32:00 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su mara baya ga kasashen yankin manyan tafkunan Afirka, wajen karfafa dunkulewarsu, da hadin gwiwar gina makomar bai daya.

Fu Cong, wanda ya yi kiran a jiya Talata, yayin zaman kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, game da batutuwan da suka shafi yankin, ya ce a shekarun baya bayan nan, kasashen yankin manyan tafkunan Afirka sun dukufa wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya, da tsaro, da samar da ci gaba, wanda hakan ya bude sabon babin farfado da zaman lafiya, tsaro, da tsarin aiwatar da hadin gwiwar raya janhuriyar dimokaradiyyar Congo da yankin manyan tafkunan Afirka.

Fu ya kuma yi kira da kasashen yankin da su karfafa tattaunawa, da yin sulhu, kana su tsaya tsayin daka wajen wanzar da zaman lafiya, su kuma yi aiki tare wajen shawo kan kalubaloli, da tabbatar da tsaron bai daya, da saukaka halin jin kai, da ingiza ci gaban bai daya.

Jami'in na Sin ya kuma bayyana aniyar kasarsa, ta goyon bayan yunkurin janhuriyar dimokaradiyyar Congo wajen kare ikon mulkin kai, da martabar yankuna, da tsaron kasa. Yana mai cewa Sin a shirye take, ta ci gaba da taka rawar gani, wajen ingiza zaman lafiya da daidaito a yankin baki daya. (Saminu Alhassan)