logo

HAUSA

Yadda Sinawa Suka Yi Hutun Mako Guda Na Bikin Zagayowar Ranar Kafa Kasar Sin

2024-10-09 07:12:13 CGTN Hausa

An kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin a ranar 1 ga Oktobar shekarar 1949, tare da bikin murnar kafa gwamnatin jama'a ta tsakiya a dandalin Tiananmen da ke sabon babban birnin kasar ta Peking wato Beijing, a wannan rana ta wannan shekarar. An gudanar da faretin farko na sabuwar rundunar 'yantar da jama'ar kasar Sin a can, biyo bayan jawabin da shugaban kasar na farko Mao Zedong ya yi, yana mai ayyana kafa Jamhuriyar a hukumance. Daga wancan lokaci ya zuwa yanzu, bikin murnar zagayowar wannan rana ya zama al’ada ga jama’ar Sinawa tare da karin hutu na kwanaki shida a kan wannan rana wanda ake kira “Golden Week” a turance. Hutun na bana ya samu gagarumin bunkasuwar yawon bude ido, tare da samun mafi yawan zirga-zirgar fasinjoji a fadin kasar.  

A al’adance a kan gudanar da bukukuwa daban-daban da gwamnati ta shirya, gami da wasannin wuta da kide-kide, da wasannin motsa jiki da al'adu. Wuraren haduwar jama'a, irin su dandalin Tiananmen a Beijing, akan kawata su bisa jigon bikin tare da hotunan shugabanni masu daraja, kamar Mao Zedong.  

Yayin da dabarun farfado da yankunan karkara na kasar Sin ke ci gaba da bunkasuwa, ingantattun ababen more rayuwa, da ayyuka masu daukar hankali sun ingiza sha’awar yawon bude ido, hakan ya sanya yankunan karkarar birnin Beijing karbar bakuncin masu yawon bude ido miliyan 4.5, wanda ya nuna karuwar kashi 13.6 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin na bara, inda kudaden da aka samu sakamakon gudanar da ayyuka masu nasaba ya kai yuan miliyan 602, wanda ya karu da kashi 4.5 cikin dari idan aka kwatanta da lokacin hutun na bara. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)