Manyan kogunan Najeriya na karkashin kulawa don dakile ambaliya
2024-10-09 11:41:11 CMG Hausa
Hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya ko NIHSA ta bayyana a jiya Talata cewa, ana kokarin daidaita yawan ruwan kogin Neja wato River Niger, daya daga cikin manyan kogunan Najeriya biyu, a wani mataki na dakile afkuwar ambaliya a kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a Afirka.
Shugaban hukumar Umar Mohammed ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce, a hankali ruwan dake cikin kogin Neja yana raguwa tun farkon wannan watan. Yana mai cewa a halin yanzu ana rage yawan ruwan madatsar ruwa ta Jebba tare da hadin gwiwa da masu gudanar da madatsar ruwar Kainji. (Mohammed Yahaya)