logo

HAUSA

Asirin Amurka a fannin tada “yakin hakkin dan Adam” a duniya

2024-10-09 21:16:16 CMG Hausa

Zuwa yau 9 ga watan Oktoba aka cika wata daya da gudanar da taro na 57 na kwamitin kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, inda kasashe sama da 100 suka bayyana goyon bayansu ga kasar Sin ta hanyoyin gabatar da jawabi tare ko daya bayan daya, wajen jaddada cewa, harkokin Xinjiang, da Hong Kong, da Xizang(Tibet), harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma bai kamata Amurka ta yi shisshigi a ciki ba. Al’amarin da ya shaida cewa, yunkurin Amurka da sauran wasu kasashe ‘yan kalilan na yammacin duniya na siyasantar da batun hakkin dan Adam, ba zai samu nasara ba.

Amurka ta kawar da ido daga matsalolin da ita kanta take fuskanta ta fannin kare hakkin Adam, kuma tana fakewa da batun hakkin dan Adam wajen matsawa sauran kasashe lamba, gami da nuna fin karfi a duniya.

Domin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, abu na farko da Amurka ta kan yi, shi ne kirkiro “laifin da ya shafi hakkin dan Adam”. Bari mu dauki kasar Venezuela a matsayin misali. A ’yan shekarun nan, bisa hujjar wai Venezuela ta aikata laifi a fannin kare hakkin dan Adam, Amurka ta fadada kakaba mata takunkumin tattalin arziki, al’amarin da ya haifar wa Venezuela matsalolin tattalin arziki da jin kai da kuma ci gaba.

Baya ga gwamnati da kafafen yada labarai, wani muhimmin abu da ya taka muhimmiyar rawa a cikin “yakin hakkin dan Adam” da Amurka ta tayar a sauran kasashe, shi ne NGO, wato kungiyoyin da ba na gwamnati ba. Wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba a Amurka, wadanda suka fake da sunan kare “demokuradiyya” da “hakkin dan Adam”, sun yi yunkurin rura wutar rikicin kawo baraka, da kulla makiricin tada rikicin siyasa, da shirga karya da sauransu a sassan kasa da kasa.

A Majalisar Dinkin Duniya kuwa, Amurka ta kan bada shawarar zartas da kudurorin kasa iri-iri ta hanyar fakewa da batun hakkin Adam, inda ta kan nuna yatsa ga wasu kasashe masu tasowa, da matsa musu lamba a fannin siyasa, kana ta kan yi yunkurin kawo cikas ga wasu batutuwan gaggawa da suka shafi jin kai.

Akasarin kasashe masu tsayawa kan adalci da gaskiya sun riga sun fahimci wayon Amurka, wato yunkurin da take na yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasar Sin da na sauran kasashe masu tasowa, ta hanyar amfani da batun hakkin dan Adam. Muryoyin kasashe sama da 100 sun shaida cewa, yunkurin da Amurka da sauran wasu kasashe ’yan kalilan suka yi, ba zai yi nasara ba. (Murtala Zhang)