Shugaban kasar Uganda ya alkawarta shiga tsakani a rikicin kasar Sudan
2024-10-09 11:37:09 CMG Hausa
Shugaba Yoweri Museveni na kasar Uganda, ya ce a shirye yake ya shiga tsakani a rikicin kasar Sudan, da tuni ya lakume rayukan dubban 'yan kasar tare da raba miliyoyi da muhallansu, muddin dai sassan dake rikicin sun amince da hakan.
Wata sanarwa da aka fitar a jiya Talata, ta ce shugaba Museveni ya yi alkawarin ne yayin da ya karbi bakuncin wakilin musamman na MDD a Sudan, Ramtane Lamamra, a ranar Litinin da ta gabata, a fadar gwamnatin Uganda dake birnin Entebbe.
Tun daga ranar 15 ga watan Afirilun bara ne, Sudan ta tsunduma cikin tashin hankali, sakamakon dauki ba dadi da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da dakarun RSF. Kawo yanzu rikicin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a kalla 16,650, tare da raba miliyoyin 'yan kasar da muhallansu. (Saminu Alhassan)