logo

HAUSA

Firaministan Sin ya yi kira da aiwatar da sauye sauyen manufofi

2024-10-09 20:52:52 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira da a yi kokarin aiwatar da sauye-sauyen manufofi domin daidaita tattalin arzikin kasar tare da kokarin cimma burin ci gaban tattalin arziki da na zaman takewa da ake tsarawa a ko wace shekara.

Li Qiang, ya bayyana haka ne jiya Talata, yayin wani taron karawa juna sani da ya kunshi masana da ’yan kasuwa, da nufin jin ra’ayoyinsu game da yanayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ciki da matakai na gaba na raya tattalin arzikin.

Firaministan ya kuma nanata bukatar sauraron bukatun kasuwa da magance damuwar da al’umma ke da ita a lokacin da ake tsarawa da aiwatar da manufofi, da ci gaba da bunkasa kwarin gwiwar samun ci gaba.

Ya ce ya kamata a yi aiki domin inganta muhallin kasuwanci da karawa harkokin kasuwanci kuzari, yana mai kira da a dauki kwararan matakan tallafawa kamfanonin dake fuskantar matsaloli da aiwatar da manufofin da suka dace da goyon bayan harkokin kasuwanci. (Fa’iza Mustapha)