Tawagar Hamas ta isa Alkahira gabanin tattaunawa da bangaren Fatah
2024-10-09 10:28:56 CMG Hausa
Wata majiya a kasar Masar ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Talata, cewa tawagar kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta isa birnin Alkahiran Masar, domin tattaunawa da takwararta ta Fatah, a wani yunkuri na warware sabanin dake tsakanin sassan biyu.
Rahotanni na cewa babban jami'in Hamas Khalil al-Hayya ne ya jagoranci wakilan bangaren kungiyarsa, ana kuma sa ran tattaunawar wadda Masar ta dauki nauyi, za ta mayar da hankali ne ga batun aiwatar da sulhu tsakanin manyan bangarorin biyu na Falasdinawa.
Kaza lika, cikin manyan batutuwan da sassan biyu za su tattauna har da yanayin da ake ciki a zirin Gaza, da makomar kan iyakar Rafah wadda ta hada Gaza da kasar Masar. Yanzu haka dai Isra’ila ce ke iko da bangaren Falasdinu na muhimmiyar iyakar.
A jiya Talata, hukumomin lafiya a Gaza sun ce ya zuwa yanzu, hare haren da sojojin Isra'ila ke kaddamarwa a Gaza sun riga sun hallaka Falasdinawa 41,965 da jikkata wasu 97,590. (Saminu Alhassan)