logo

HAUSA

Dorewar bunkasuwar tattalin arzikin Sin ta karawa duniya kwarin gwiwa

2024-10-09 10:28:07 CMG Hausa

 

Tattalin arzikin Sin na samun bunkasuwa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba a watannin da suka gabata, bayan jerin matakai masu nasaba da gwamnatin kasar ke dauka, matakin da ya kyautata kiyasin kasuwa.

Kwanan baya, Goldman Sachs, da UBS, da kuma Morgan Stanley da dai sauran cibiyoyin zuba jari, sun bayyana kwarin gwiwarsu game da makomar dukiyoyin kasar Sin, inda hukumomi da dama suka daga matsayin darajar takardun hannun jarin Sin.

A matsayinta na kasa mai karfin tattalin arziki na biyu a duniya, ci gaban tattalin arzikin Sin ya karfafa kwarin gwiwar dukkanin fadin duniya. A halin yanzu, ana fuskantar yanayin siyasa mai sarkakiya a wasu wurare, inda ake fuskantar raunin farfadowar bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya gabatar da kiyasin cewa, yawan bunkasuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 3.2%, adadin da ya kasa na bara. Lura da hakan, ba shakka dorewar ci gaban tattalin arzikin Sin a baya bayan nan, karfi ne, kuma kyakkyawan fata ne ga farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)