Magatakardar MDD ya yi gargadin cewa kasar Lebanon na gab da shiga yaki mai tsanani
2024-10-09 10:44:27 CMG Hausa
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana a ranar Talata cewa, kasar Lebanon na gab da shiga yaki gadan-gadan.
Ya ce, a cikin 'yan kwanakin nan da suka gabata, musayar wuta tsakanin Hizbullah da sauran kungiyoyin gwagwarmaya a kasar Lebanon da dakarun tsaron Isra'ila na ci gaba da kara kamari a iyakar Lebanon da Isra'ila da tuddan Golan, tare da yin watsi da kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1701 da 1559.
Babban jami'in na MDD ya nanata kiraye-kirayen tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza da Lebanon, da gaggauta sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ba tare da wani sharadi ba, da ba da tallafin ceton rayuka ga duk wadanda ke cikin tsananin bukatarsa, da kuma yin kira da a dauki dauwamamman matakin samar da kasashe biyu tsakanin Isra'ila da Falasdinu. (Yahaya)