logo

HAUSA

Tsohon shugaban Nijar Issoufou Mahamadou zai halarci dandalin ci gaban Afrika a Kigali

2024-10-08 11:02:41 CMG Hausa

Tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou a matsayinsa na shugaban Zlecaf ya sauka a ranar jiya Litinin 7 ga watan Oktoban shekarar 2024 a babban birnin Kigali na kasar Rwanda bisa goron gayyatar shugaban kasar Paul Kagame.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada a turo mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan rangadin aiki na tsohon shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou zuwa kasar Rwanda, ya biyo bayan ziyarar aiki da ya kai a kasar Senegal tare da ganawa da shugaban kasar Bassirou Diomaye Faye cikin tsarin rangadinsa na matsayin shugaban kwamitin koli domin ci gaba da tsaro a kasashen yankin Sahel.

Wannan ziyara, a birnin Kigali na kasar Rwanda, na bayyana sanarwar dake tabbatar da tsohon shugaban kasar Nijar a matsayin manzon musamman da zai yi jawabi a wannan karo na dandalin Biashara Afrika Business Forum na AFCTA bisa goron gayyatar shugaba Paul Kagame na kasar Rwanda da zai gudana a birnin Kigali daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Oktoban shekarar 2024.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.