AU ta taya Taye Atske Selassie murnar zama sabon shugaban kasar Habasha
2024-10-08 10:56:16 CMG Hausa
Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka ko (AU) Moussa Faki Mahamat a jiya Litinin, ya taya Taye Atske Selassie murnar nadinsa da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Habasha.
A jiya Litinin din ne majalisun dokokin kasar Habasha suka nada ministan harkokin wajen kasar Taye Atske Selassie a matsayin sabon shugaban kasar. Nadin ya biyo bayan karewar wa’adin shugabar kasar mai ci Sahle-Work Zewde ne, bayan shafe shekaru shida tana shugabancin kasar.
Faki ya kuma yabawa Zewde, wacce ke kan karagar mulki tun watan Oktoban shekarar 2018 a matsayin mace ta farko da ta yi shugabancin kasar, "da kuma jagorancinta mai cike da tarihi da tasiri a tsawon shekaru shida da ta yi tana shugabancin kasar."
Ya kuma kara nanata ci gaba da goyon bayan kungiyar AU ga yunkurin kasar Habasha na zurfafa dimokaradiyya da ci gaba mai dorewa. (Yahaya)