logo

HAUSA

Fu Cong: Kasar Sin tana goyon bayan MDD don kara himma da inganci

2024-10-08 11:09:24 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya FU Cong ya bayyana jiya Litinin cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da dukkan bangarori wajen marawa MDD baya don ta kara himma da inganci, da kuma tabbatar da an aiwatar da alkawuran siyasa na yarjejeniyar taron makomar duniya, da gina al'umma mai makomar bai daya ga bil'Adama, da rungumar kyakkyawar makoma ga kowa da kowa.

Ya ce, al’ummar kasashen duniya sun yi kira da a samar da duniya mai daidaito, kwanciyar hankali da dorewa, kuma suna fatan MDD za ta kara taka muhimmiyar rawa wajen cimma wannan buri.

Fu ya bayyana cewa, gaggauta aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030 ita ce manufar taron koli kan makomar duniya, kuma yarjejeniyar makomar duniya ta dora muhimmanci kan ajandar ci gaba, tana mai tabbatar da ka'idar bai daya amma mabambantan matakai a sassa daban-daban na ci gaba, da kuma bayyana alkiblar sake fasalin tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa.  (Mohammed Yahaya)