Mutane 7 sun rasu kana wasu 59 sun jikkata sakamakon harin makamai kan sansanin ‘yan gudun hijira a yammacin Sudan
2024-10-08 11:05:07 CMG Hausa
Babban darakta a hukumar kiwon lafiya ta jihar Dafur ta Arewa Ibrahim Khatir, ya tabbatar da kisan mutane 7, da jikkatar wasu mutane 59, sakamakon harin makaman atilare da dakarun RSF suka kai kan sansanin wadanda suka tserewa muhallansu dake birnin El Fasher, na jihar Dafur ta Arewa a yankin yammacin kasar Sudan.
Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho, Khatir ya ce, sansanin tsugunar da jama’a na Abu Shouk ya fuskanci hari a ranar Lahadi, wanda ya hallaka mutane 2 da jikkata mutum 20, da kuma wani harin na daban a jiya Litinin, wanda ya haifar da rasuwar mutane 5 da jikkatar mutane 39.
Tuni dai kungiyar likitoci ta “Sudanese Doctors Network”, ta yi Allah wadai da harba makamai kan matsugunan fararen hula, tana mai cewa hakan ya kara kazanta halin kunci da wadanda suka kauracewa gidajensu, da fararen hula ke ciki, wadanda tuni suke cikin mawuyacin halin matsin rayuwa, sakamakon kawanya da mayaka suka yiwa birnin. (Saminu Alhassan)