Shirin samar da abinci na duniya WFP ya sabunta yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin jihar Borno
2024-10-08 11:03:57 CMG Hausa
Gwamnan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya bukaci karin samun tallafi daga shirin samar da abinci na duniya ta yadda jihar za ta hanzartar samun murmurewa daga mummunan tasirin annobar ambaliyar ruwa da ya faru kwanan nan.
Ya bukaci hakan ne jiya Litinin 7 ga wata a gidan gwamnatin jihar dake birnin Maiduguri lokacin da ya karbi bakuncin babbar daraktar shirin na WFP Mrs Cindy McCain.
Daga tarayyar najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya shaidawa tawagar shirin na WFP cewa, ambaliyar da jihar ta fuskanta a kwanakin baya ya cinye gine-gine da dama, sanann kuma ya karya gadoji tare da lalata tituna wanda ya yi sanadin raba garuruwa da dama. Ya kuma yabawa da kokarin shirin samar da abincin na duniya bayar da taimakonsa tun daga lokacin da jihar ta yi ta fuskantar hare-haren ’yan ta’adda da kuma taimakon jin kai na baya-bayan nan ga mutanen da annobar ambaliyar ruwa ta shafa.
Haka kuma gwamnan jihar Borno ya yi kira ga shirin samar da abincin na MDD da ya taimakawa jihar ta fuskar bunkasa sha’anin noman rani ga manoman da suke zaune a yankunan da suke da ruwa, ta hanyar samar musu da ingantattun irin shuka da fanfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana.
A jawabinta bayan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, darakta janaral ta shirin samar da abinci ta duniya Mrs Cindy McCain ta jaddada cewa, wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Borno ta hanyar kyautata dabarun samar da wadataccen abinci a jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)