Akwai bukatar kasashen duniya su kira babban taron tattauna batun wanzar da ingantaccen tsaro
2024-10-08 20:19:54 CMG Hausa
Yayin da aka cika shekara 1 da barkewar rikicin Gaza a jiya 7 ga wata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta ce shaidu sun nuna cewa, matakan soji da rikici, ba su ne hanyoyin warware matsala ba, sai dai kara nisanta da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Mao Ning ta bayyana haka ne yau Talata, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, inda ta ke mayar da martani ga tambayoyin ’yan jaridu.
A cewarta, ya kamata a tabbatar da halaltattun hakkokin kasa na al’ummar Palasdinu, haka kuma a dauki damuwar da Isra’ila ke da ita don gane da tsaronta da muhimmanci. Ta kara da cewa, ya kamata duniya ta kira wani babban taron tattauna zaman lafiya na kasa da kasa mai inganci da karfin iko, tare da tsara jadawalin aiwatar da tsarin kafa kasashe biyu da tabbatar da zaman jituwa tsakanin Isra’ila da Palasdinu da ma Larabawa da Yahudawa, da zummar yayyafa yanayin da ake ciki ruwan sanyi.
A martaninta game da batun Lebanon, Mao Ning ta bayyana cewa kasar Sin ta shirya rukunoni 2 na aikin kwashe Sinawa 215 daga Lebanon ta jiragen ruwa da na sama da aka yi shata, cikinsu har da ’yan Hong Kong 3 da na Taiwan 1. Ta kara da cewa, bisa bukatar gwamnatin Lebanon, gwamnatin Sin ta yanke shawarar samar da kayayyakin agajin gaggawa na kiwon lafiya ga kasar domin taimaka mata gudanar da ayyukan kiwon lafiya. (Fa’iza Mustapha)