logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Colombia zai ziyarci kasar Sin

2024-10-08 19:42:04 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Colombia Luis Gilberto Murillo, zai ziyarci kasar Sin daga ranar 9 zuwa 12 ga watan nan na Oktoba.

Bisa sanarwar da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta yi a yau, ministan zai kawo ziyarar ne bisa gayyatarsa da takwaransa na Sin kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS Wang Yi ya yi. (Fa’iza Mustapha)