Firaministan kasar Sin zai halarci jerin taruka tare da ziyartar Laos da Vietnam
2024-10-08 19:30:18 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci taro karo na 27 tsakanin Sin da kasashen ASEAN, da taro karo na 27 na kasashen ASEAN da wasu karin kasashe 3 da kuma taro karo na 19 na kasashen gabashin Asia da za su gudana a Vientiane na Laos daga 9 zuwa 12 ga watan nan na Oktoba. Haka kuma zai yi ziyarar aiki a Laos din.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ce ta sanar da haka a yau Talata, inda ta ce firaministan zai kuma yi ziyarar aiki a Vietnam daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Oktoba. (Fa’iza Mustapha)