Yadda birnin Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza ya kasance bayan rikici
2024-10-08 16:25:55 CMG Hausa
Yadda birnin Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza ya kasance a yanzu ke nan. Alkaluman da hukumar lafiya ta zirin Gaza ta samar sun shaida cewa, bayan barkewar rikici a tsakanin Palasdinu da Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban bara, al’ummar Palasdinu kusan dubu 42 sun halaka sakamakon matakan soja da Isra’ila ta dauka a zirin Gaza, baya ga sama da dubu 97 da suka jikkata.(Lubabatu)