Sin za ta samarwa Lebanon tallafin jin kai cikin gaggawa
2024-10-08 14:03:53 CMG Hausa
Mai magana da yawun hukumar hadin kai da samun bunkasuwa tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin Li Ming ya bayyana a yau Talata cewa, halin da Labanon ke ciki a kwanakin nan na kara tsananta, ta yi fama da fashewar bama-bamai da aka dasa cikin na’urorin sadarwa da kuma hare-hare daga sama, lamarin da ya yi sanadin asarar mutane da dama. Bisa bukatun gwamnatin Lebanon, gwamnatin Sin ta yanke shawarar samarwa kasar tallafin jin kai na jinya cikin gaggawa, don taimakawa kasar wajen gudanar da aikin ceto da ba da jinya. (Amina Xu)