Tawagar sojojin kasar Sin dake tabbatar da zaman lafiya a Sudan ta kudu ta ci jarrabawar da sashen MDD dake kasar ta shirya mata
2024-10-07 07:17:48 CGTN Hausa
A kwanan baya, a karo na biyu a shekarar 2024, kungiyar MDD da aka jibge a kasar Sudan ta kudu da yankin yaki na Juba ta tantance karfin yaki na tawagar sojojin kasa ta kasar Sin ta 10 wadda ke tabbatar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu kan yadda take samun horo a yau da kullum, da sauke nauyin dake bisa wuyanta da ba da tabbaci wajen samar da kayayyakin soja da ake bukata da dai makamatansu. Daga karshe dai, wannan tawagar kasar Sin ta samu kyakkyawan maki. (Sanusi Chen)