Zirga-zirgar ababen hawa na gudana yadda ya kamata yayin hutun mako guda na Sin
2024-10-07 21:04:32 CMG Hausa
Ofishin kula da zirga-zirgar ababen hawa na ma’aikatar kula da tsaron al’umma ta kasar Sin, ya ce yayin da hutun mako guda na bikin ranar kafuwar sabuwar kasar Sin ke zuwa karshe, adadin matafiya masu dawowa daga bulaguro ya fara karuwa a jiya Lahadi, amma duk da haka babu wata matsala ko cunkoso don gane da yanayin zirga-zirgar ababen hawa.
Alkaluma daga ma’aikatar kula da sufuri ta kasar Sin sun nuna cewa, daga ranar 1 zuwa 4 ga wata, adadin fasinjojin da suka yi zirga-zirga tsakanin yankunan kasar ya zarce biliyan 1.1. Baya ga haka, ta yi hasashen adadin wadanda suka tuka mota domin bulaguro zuwa yawon shakatawa a lokacin hutu tsakanin 1 zuwa 7 ga watan Oktoba, zai kai biliyan 1.5. (Fa’iza Mustapha)