logo

HAUSA

Sin ta bukaci a yi bincike tare da hukunta wadanda suka kai wa motocin kamfanin kasar hari a Pakistan

2024-10-07 20:26:14 CMG Hausa

Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a Pakistan, wanda ya yi sanadin mutuwar Sinawa biyu da ma wasu ‘yan kasar Pakistan. Haka kuma ta jajantawa wadanda suka jikkata, da ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ne ya bayyana haka a yau, lokacin da yake amsa tambaya game da harin da aka kai wa motocin wani kamfanin kasar Sin a Pakistan, a jiya Lahadi.

A cewar kakakin, Sin na bukatar Pakistan ta yi dukkan kokarin da ya kamata domin jinyar wadanda suka jikkata tare da aiwatar da cikakken bincike don kama wadanda ke da hannu da kuma tabbatar da sun fuskanci fushin doka.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan Pakistan wajen inganta ayyukan yaki da ta’addanci, kuma a shirye take ta hada hannu da Pakistan din wajen dakile duk wani yunkuri na lalata dangantakar dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)