logo

HAUSA

Afirka ta Kudu: Za a mika daukacin shaidu kan kisan kiyashi da Isra'ila ta yi

2024-10-07 15:41:47 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu Ronald Lamola ya bayyana a jiya Lahadi cewa, gwamnatin kasarsa za ta mika dukkan shaidu dangane da kisan kare dangi da kasar Isra'ila ta yi wa Falasdinawa, ga kotun kasa da kasa ta Majalisar Dinkin Duniya, kafin karshen watan da muke ciki.

A cewar Mista Lamola, za a samar da cikakken bayanin da likitoci suka tsara, don bayyana yanayin wasu ayyukan ta'addanci da aka yi a yankin Gaza. Yana mai cewa, ta haka za a tabbatar da laifin kasar Isra'ila na neman kawar da daukacin al'ummar Falasdinawa ta hanyar kisan kiyashi.

Da ma a watan Disamban shekarar 2023, kasar Afirka ta Kudu ta kai kara kotun kasa da kasa, tana zargin kasar Isra'ila da aikata kisan kare dangi a yankin Gaza. Daga baya, a watanni Janairu da na Maris na bana, kotun ta gabatar da wasu matakai na wucin gadi, inda ta bukaci bangaren Isra'ila da ya bi dokar kaucewa aikata kisan kare dangi, gami da daukar duk wani matakin da ya wajaba, don tabbatar da ganin shigar kayayyakin tallafin jin kai cikin zirin Gaza yadda ake bukata. (Bello Wang)