Motar dakon kayan sabon makamashi
2024-10-06 14:27:59 CMG Hausa
An fara yin amfani da manyan motocin dakon kaya dake aiki da sabon makamashi mai tsabta a birnin Tangshan na lardin Hebei na kasar Sin domin rage fitar da hayaki mai kunshe da sinadarin carbon. Kawo yanzu adadin motocin da ake amfani da su a birnin ya riga ya kai sama da 14200. (Jamila)