logo

HAUSA

Kudin Sin da ake cinikayyar waje da shi ya karu da sama da kaso 20% cikin watanni 8 na farkon bana

2024-10-05 16:12:58 CMG Hausa

Wani rahoto da babban bankin kasar Sin ya fitar ya nuna karuwar adadin kudin Sin RMB, da ake cinikayyar waje da shi, da sama da kaso 20 bisa dari cikin watanni 8 na farkon shekarar nan ta 2024, yayin da kudin na Sin ke kara samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa.

Rahoton babban bankin na Sin game da yadda kudin kasar Sin RMB ke kara shiga sassan kasa da kasa ta fuskar cinikayya, da biyan kudade, ya nuna yadda hakan ya fadada zuwa kaso 21.1 bisa dari cikin shekara guda, zuwa kudin Sin yuan tirliyan 41.6, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 5.94 a tsakanin watannin Janairu da Agustan bana.

Rahoton ya ce cikin wa’adin na watanni 8, adadin kudin Sin RMB da aka yi amfani da shi wajen biyan kudade, da sayen hajojin cinikayya ya kai kaso 26.5 bisa dari na jimillar kudaden gida da na waje da aka kashe, wajen musayar kudaden waje, karuwar da ta kai ta kaso 24.8 bisa dari kan na shekarar 2023.

A fannin bayar da hidimomi kuwa, amfani da RMB tsakanin sassan kasa da kasa ya karu da kaso 22.3 bisa dari a shekara zuwa yuan tiriliyan 1.2, kudaden da suka kai kaso 31.8 bisa dari cikin jimillar adadin. (Saminu Alhassan)