logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga kwamitin tsaron MDD da kada ya yi watsi da bincike game da fashewar bututun gas na Nord Stream

2024-10-05 15:46:56 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga kwamitin tsaron MDD da kada ya yi watsi da bincike, game da fashewar bututun iskar gas din nan na Nord Stream, kana kada kwamitin ya kawar da kai, ko yin fuska biyu game da binciken lamarin.

Shekaru biyu ke nan da suka wuce, aka samu aukuwar fashewar bututun iskar gas na Nord Stream dake shimfide a tekun Baltic, wanda hakan ya haifar da mummunan tasiri ga hada hadar makamashi ta duniya, da kalubale ga yanayin muhallin halittun ruwa, da tsaron jiragen ruwa na dakon hajoji.

Geng Shuang, wanda ya yi tsokacin yayin zaman kwamitin tsaron game da batun bututun nan Nord Stream, ya kara da cewa, cikin shekaru 2 da suka gabata, sassan kasa da kasa na ta bibiyar ci gaban binciken da ake yi don gane da wannan lamari, kuma kwamitin tsaron ya kammala tattaunawa daban daban, inda da yawa daga mambobin kwamitin ke ci gaba da kiraye-kirayen yin adalci, da kaucewa nuna son kai, da neman kwararru masu bincike su gaggauta gabatar da gaskiyar abun da ya faru, tare da hukunta masu hannu cikin aikata wannan ta’asa. To sai dai kuma abun takaici a cewar jami’in har yanzu ba a kai ga karshen wannan batu ba.

Game da kudurin da aka gabatar yayin zaman, wanda Geng ya bayyana da mai kunshe da adalci, wanda kuma ya tattaro damuwar dukkanin sassa, bisa daidaito, ya yi fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a wannan batu za su kara azamar tattaunawa, da gaggauta cimma yarjejeniya game da daftarin, ta yadda za a iya aikewa duniya wani sahihin sako game da wannan muhimmin batu.  (Saminu Alhassan)