logo

HAUSA

An ji dadin wasannin nuna kayayyakin tarihin da aka gada daga kaka da kakani a birnin Emeishan

2024-10-05 14:30:00 CMG Hausa

A daren ranar 2 ga wata, an nuna kayatattun wasannin fasaha a birnin Emeishan na lardin Sichuan da ke kasar Sin, inda aka nuna wa mazauna wurin da masu yawon bude ido kayayyakin tarihin da aka gada daga kaka da kakani iri daban daban fiye da 10, kamar su wasan Kongfu na Emei, wasan rawar ciyayi mai siffar dabbar dragon, wasan rawa ta kabilar Miao tare da busa kayan kida na Lusheng, da dai sauransu.