Sin na fatan warware takaddamar cinikayya da Turai game da EV ta hanyar cimma alkawarin farashi
2024-10-05 20:12:05 CMG Hausa
Kasashe mambobin kungiyar EU, sun zartas da kudurin kara haraji kan motoci masu aiki da lantarki ko EVs kirar kasar Sin, bayan jefa kuri’a a jiya Jumma’a. Game da hakan, hukumar inganta cinikkayar kasar Sin ta bayyana cewa, tana tsaye tsayin daka kan adawa da karin harajin Turai kan motocin na EVs kirar Sin.
Kamfanonin kirar motoci masu aiki da lantarki na Sin, sun dade suna nuna cikakkiyar niyyar su ta amsa bincike daga bangaren Turai, tare da fatan warware takaddamar cinikayya game da motoci masu aiki da lantarki tsakanin Sin da Turai cikin lumana, ta hanyar cimma alkawarin farashi, da sauran hanyoyin da suka dace bisa ka'idodin kungiyar WTO. (Safiyah Ma)