Dimokuradiyyar jama'a da ta shafi matakai daban daban wani muhimmin tabbaci ne ga ci gaban kasar Sin
2024-10-04 16:01:18 CMG Hausa
"A cikin shekaru 75 da suka gabata, jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ta hada kai tare da jagorantar al'ummun dukkan kabilun kasar Sin, wajen kokarin samar da manyan ababen ban mamaki guda biyu: wato saurin bunkasuwar tattalin arziki, da zaman lafiyar al'umma cikin dogon lokaci." Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya takaita nasarorin da sabuwar kasar Sin ta samu, a yayin wata liyafar da aka gudanar kwanan nan, don murnar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin.
To ko me ya sa kasar Sin ta iya cimma irin wadannan nasarori? Dimbin masu nazarin al'amuran kasa da kasa na kokarin neman amsar wannan tambaya, ta hanyar nazari kan tsarin dimokuradiyya ta Sin, da ingancin ayyukan gudanar da mulki a kasar. Daga tunani na mai da moriyar jama'a a gaban komai, har zuwa tsarin dimokuradiyyar jama'a da ya shafi matakai daban daban, inda sannu a hankali aka fara fahimtar tunani mai zurfi da ya tabbatar da ci gaban kasar Sin.
Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, an kafa wasu muhimman tsare-tsare na siyasa a kasar, kamarsu tsarin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, da tsarin hadin gwiwar jam'iyyu da dama, da kuma tattaunawa kan al'amuran siyasa, ta yadda aka samu tabbaci kan cewar "Dukkan ikon mulki a jamhuriyar jama'ar kasar Sin na karkashin mallakar al'ummar kasar." Kana a nasa bangare, tsarin dimokuradiyyar jama'ar kasar Sin mai kunshe da matakai daban daban, ya tabbatar da haduwar fannonin ayyuka da sakamako, da tsari na kai tsaye da na kaikaice, da ra'ayin jama'a da manufar kasa.
Dimokuradiyya nau'i nau'i ce, ba wai salo daya ce kadai, wato salon kasashen yamma ba. Kana ita dimokuradiyya ba kayan ado ba ne. Ana amfani da ita ne don daidaita matsaloli da biyan bukatar jama'a. Wannan tunani ya sa tsarin dimokuradiyya ke taka muhimmiyar rawa a ci gaban harkoki daban daban na kasar Sin. (Bello Wang)