logo

HAUSA

Wakilin Sin: Ya kamata a kiyaye da karfafa gudummawar MDD a fannin yaki da ta'addanci

2024-10-04 16:23:18 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana jiya Alhamis cewa, ya kamata a aiwatar da kudurin yaki da ta’addanci na kwamitin sulhu da babban taron MDD, da tsare-tsaren yaki da ta’addanci na kasa da kasa na MDD, tare da yaki da kungiyoyi, da mutane masu tallafawa ta’addanci dake cikin jerin da kwamitin sulhu ya fitar, ta yadda za a kiyaye, da karfafa babbar gudummawar MDD a fannin gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin kasa da kasa domin yaki da ta’addanci.

A dai jiyan, kwamiti na shida na babban taron MDD ya gudanar da taro mai taken “matakan kawar da ta’addanci na kasa da kasa”. Kuma cikin jawabin da ya gabatar yayin zaman, Geng Shuang ya ce a halin yanzu, ana samun barkewar tashe tashen hankula da yake yake, kuma ra'ayin ta’addanci ya sake farfadowa. Don haka bangaren Sin ya fitar da wasu matakai na yaki da ra’ayin ta’addanci tsakanin kasa da kasa:

Na farko, ya kamata a tsaya tsayin daka kan hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban. Na biyu, ya kamata a tsaya tsayin daka ga kare dokokin kasa da kasa, wato ya kamata ayyukan yaki da ra’ayin ta’addanci su bi ka’idoji da tsarin dokokin MDD. Na uku, ya kamata a tsaya tsayin daka kan gudanar da matakai a dukkan fannoni. Ya kamata yaki da ta’addanci ya dora muhimmanci kan samar da ci gaba, don wargaza muguwar alakar dake akwai tsakanin talauci da ta'addanci. Na huda, ya kamata a tsaya tsayin daka kan inganta matakan yaki da ta’addanci. Ya kamata bangarori daban daban su karfafa mu’ammala da juna, don taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta karfin yaki da ta’addanci.  (Safiyah Ma)