Sin na goyon bayan gaggauta aiwatar da shawarar cimma gajiya daga fasahohin dijital
2024-10-04 19:59:07 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce kamata ya yi a kara azamar samar da damammakin yada fasahohi, da kwarewar makaman aiki ga kasashe masu samun saurin ci gaba da masu tasowa, don cimma nasarar kawar da wagegen gibin fasahohin dijital, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba, wajen cin gajiyar sauyin fasahohi, da cimma nasarar tafiya tare ta fuskar tsara manufofi.
Dai Bing wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin babban taron muhawara game da batutuwan raya zamantakewar al’umma karkashin zaman kwamiti na 3 na babban zauren MDD, ya ce Sin na goyon bayan gaggauta aiwatar da shawarar da MDD ta amincewa, game da cimma gajiya daga fasahohin dijital tsakanin kasa da kasa ta hanyoyin da suka dace.
Ya ce karancin mayar da hankali, da samar da isasshen jari ne ginshikan tafiyar hawainiya da ake samu a fannin bunkasa zamantakewar al’ummun duniya. A hannu guda kuma, kasar Sin na kira da a dora muhimmanci kan manufofin siyasa don su kasance ayyuka na hakika, na dora ci gaban zamantakewar al’ummu kan turba ta gari. (Saminu Alhassan)