logo

HAUSA

Sin na adawa da kara haraji da EU ta yi kan motoci masu aiki da lantarki kirar Sin

2024-10-04 20:26:28 CMG Hausa

Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, ya amsa tambayoyin dan jarida game da kudurin kara haraji kan motoci masu aiki da lantarki ko EVs kirar kasar Sin da kungiyar EU ta zartas bayan jefa kuri’a. 

Kakakin ya ce bangaren Sin ya tsaya tsayin daka kan nuna adawa da matakin ba da kariyar cinikayya daga bangaren Turai bisa rashin adalci, da rashin bin ka'ida a cikin kudurin. Kaza lika yana bayyana adawa da kara haraji da bangaren Turai ya yi kan motocin EVs kirar Sin dake shiga Turai daga kasar Sin. 

Jami’in ya ce kasar Sin ta bukaci bangaren Turai da ya tabbatar da manufarsa ta siyasa, da komawa kan hanyar tattaunawa ta warware sabanin cinikayya. Bugu da kari, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan kare moriyar kamfanoninta yadda ya kamata. (Safiyah Ma)