Shugaban Najeriya ya bukaci a gudanar da bincike tare da daukar mataki a kan musabbabin hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger
2024-10-04 14:49:32 CMG Hausa
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci hukumomin da suke da ruwa da tsaki a kan harkar sufurin ruwa, da su gaggauta gudanar da bincike a kan musabbabin hadarin jirgin ruwa a jihar Niger, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Shugaban ya bukaci hakan ne ranar Alhamis 3 ga wata a cikin sakon sa na jaje ga gwamnati da al'ummar jihar Niger a kan abun da ya faru a farkon wannan makon.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Kamar dai yadda yake kunshe cikin wata sanarwa wadda take dauke da sa hannun mashawarcin shugaban na Najeriya kan harkokin yada labaru Bayo Onanuga, shugaban na Najeriya ya ce ya kadu mutuka bisa samun rahoton hatsarin jirgin ruwan wanda ya faru a daren Talatar da ta gabata.
Shugaban ya baiwa hukumar lura da sufurin ruwa na cikin gida umarnin gudanar da bincike a kan abubuwan da suke haifar da yawaitar hadarurrukan jiragen ruwa a sassan daban daban na Najeriya, tare kuma da fito da hanyoyin masu inganci da za su kawo karshen wannan annoba.
Ha ila yau ya bukaci hukumar da ta fadada ayyukan sanya ido a dukkannin madatsun ruwan kasar, domin tabbatar da ganin cewa matafiya masu amfani da jiragen ruwa sun sami cikakkiyar kariya, tare kuma da ganin cewa ana bin dokokin da suke da nasaba da sufurin ruwa .
Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya yaba mutuka bisa kokarin ma'aikatan ba da agaji na hukuma, da na masu zaman kansu, bisa namijin kokarin da suka yi wajen ceto da dama daga cikin mutanen da hatsarin jirgin ruwan na jihar Niger ya ritsa da su, ya kuma yi fatan Allah ya kare afkuwar hakan a nan gaba.(Garba Abdullahi Bagwai)