logo

HAUSA

Sin ta bukaci kwamitin sulhun MDD da ya ingiza sassauta rikicin Lebanon da Isra’ila

2024-10-03 16:45:45 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a taron gaggawa na tattauna yanayin Lebanon da Isra’ila na kwamitin sulhun MDD jiya Laraba cewa, a halin da ake ciki, ya zama dole kwamitin sulhun MDD ya dauki matakai cikin gaggawa don samar da mafita mai tabbaci da gaskiya, kuma ya sa kaimi ga sassauta rikicin Lebanon da Isra’ila cikin gaggawa, ya yi iyakacin kokarin hana yaduwar yakin, ya kuma yi kira da bangarorin da abin ya shafa su warware matsalar ta hanyar siyasa da diflomassiya.

Bangaren Sin ya bayyana cewa, a cikin makwanni biyu da suka gabata, an tsananta yanayin yanakin Gabas ta Tsakiya, musamman ma halin da ake ciki a Lebanon. Bangaren Sin ya matukar damu da yanayi mai tsanani da ake ciki yanzu da kuma makomar yankin. Bangare Sin ya yi kira da a mutunta ‘yancin kasa, tsaro da cikakkun yankunan kasa na kasashe daban daban, ya nanata ra’ayinsa game da adawa da dukkan ayyukan keta ka’idojin dangantakar kasa da kasa, da yin Allah wadai da dukkan ayyukan kai hare-hare ga fararen hula. Bangaren Sin ya yarda da matsayin MDD, wato dukkan ayyukan Isra’ila na kutsa kai cikin Lebanon ba bisa doka ba sun keta ikon mulkin kasa da cikakkun yankunan kasar na Lebanon, wadanda suka keta ka’idoji na kuduri mai lambar 1701 na kwamitin sulhu.

Bangaren Sin ya jadadda cewa, halin da ake ciki a yankin yana ta kara tsananta, ya dace a dauki mataki nan da nan. Bangaren Sin na fatan manyan kasashe dake da tasiri za su sauke nauyin dake wuyansu, su ba da gudummawarsu don hana habakar rikicin da yankin ke ciki. (Safiyah Ma)