Rayuwar Aikin Koyar Da Kwallon Kafa A Kasar Sin
2024-10-03 20:15:43 CMG Hausa
Yayin da kasar Sin ke kara samun tagomashi ta fuskar raya wasanni, wani matashi dan asalin kasar Zimbabwe mai suna Ruramai Gillian Chakuzira, ya ce shekaru 7 ba su ishe shi samun cikakkun labarai masu kayatarwa game da kasar Sin ba, musamman batutuwan da suka shafi cinikayya, tattalin arziki, da kwallon kafa wadda yake matukar kauna.
Tun kafin zuwan sa kasar Sin a shekarar 2017, Chakuzira ya jima yana buga kwallon kafa, kuma har bayan isowarsa jami’ar Huzhou ta lardin Zhejiang na gabashin kasar Sin domin karatun digirin farko ya ci gaba da buga kwallo.
Da yake tsokaci game da yadda ya tarar da kasar Sin, matashin ya ce "Na yi tafiye tafiye zuwa wurare da dama a duniya, na kuma lura cewa Sin wata babbar cibiya ce ta sarrafa hajoji, da kuma kasuwancin fitar da su zuwa ketare. Buri na shi ne samun damar fahimtar wannan kasa, da kuma samun digirin farko a fannin cinikayyar kasa da kasa”.
A ko da yaushe, Chakuzira na da burin gabatar da abubuwan da ya koya a kasar Sin zuwa kasarsa ta haihuwa, amma a daya hannun yana fatan ci gaba da zama a kasar Sin domin samun karsashi, da nishadantuwa, da more kyakkyawan yanayin kasar.
A shekarar 2022, Chakuzira ya buga kwallo a birnin Beijing, a kuma lokacin ne ya hadu da mista Li Feiyu, darakta a kungiyar kwallon kafa ta Longding Yiya. Kuma bayan sun dan tattauna Chakuzira ya amince ya horas da yara kanana dake koyon kwallon kafa a kungiyar.
Game da hakan, Chakuzira ya ce "Shawara ce mai sauki na yanke. Na lura da bunkasar wasan kwallo a kasar Sin, kuma yara da dama suna son buga wasan kwallo. Don haka na amince na dawo birnin Beijing. Kaza lika, ina sha’awar shiga wani abu dake dunkule kwallon kafar Sin da sauran al’adun kwallon kafa na kasar wuri guda, don ganin ko za mu iya samar da wani sabon abu daga hakan".
Ya zuwa yanzu, Chakuzira mai shekaru 29 a duniya ya riga ya buga kwallo ta tsawon shekaru 25. A gida Zimbabwe, kocin sa ya karfafa masa gwiwar karantar wasan kwallo, ta yadda zai iya fahimtar wasan sosai ba kawai buga kwallo kadai ba, wanda hakan ya ba shi damar zama dan wasa kuma koci mai kwarewa.
A cewar sa "Ana iya samun koci mai shekaru 60 da wani mai shekaru 20, kuma dukkanin su na iya koyar da wani sabon abu mai kayatarwa. Kuma wannan shi ne abu mai ban sha’awa game da kwallon kafa”.
Kungiyar kwallo ta yara da Chakuzira ke horaswa na kunshe da yara ‘yan shekaru 13 zuwa 15, mafi yawan su ‘yan shekaru 5 zuwa 12. Kuma suna samun horo sau 3 a duk mako, tare da buga wasa daya a duk mako, ko wanne wasa daya cikin sa’o’i 2. Chakuzira yana kimanta baiwa daidaikun yaran horo, wanda hakan a ganin sa yana taimakawa yaran su samu kwarewa da za ta ba su damar taimakawa nasarar kungiyar su.
A cewarsa "Hakan tamkar gina gida ne, ba zai yiwu a yi gini da bulo daya ba. Dole a sanya bulo masu yawa, kuma ko wane bulo dole ya zama mai kwari. Yin komai yadda ya kamata shi ne ke jagorantar matasan ‘yan wasa zuwa ga koyon mika kwallo, da bugun tazara, da sauran dabarun sarrafa kwallo. Kwazo, da nacewa, da aiki tukuru, dukkanin su abubuwa ne masu kyau da ake koya a wasan kwallon kafa, wadanda kuma ke da amfani a sauran sassan rayuwa, da taimakawa ga cimma nasara".
Cikin shekaru 2 da suka gabata, Chakuzira yana cike da jin dadin ganin yadda yara Sinawa ke bunkasa kwarewar su ta fuskar kwallon kafa, tun daga matakin farko na buga kwallo da kyar, har zuwa gwada fasahohin taurarin su na kwallon kafa. Ya ce “Ko kadan ba su da niyyar barin wasan”.
Wannan lokaci ne dake tuna masa da lokacin yarintarsa a Zimbabwe. A ta bakinsa "Ina da a kalla abokai na kusa 20, kuma cikin mintuna 5 ina iya gayyatar 10 daga cikin su mu buga kwallo nan da nan. Amma yaran kasar Sin suna da abubuwa da dama da ayyuka masu yawa, ba abu ne mai sauki gare su su taru su yi wasa ba, don haka a lokutan da muke yin atisaye, ina ba su damar nishadantuwa da kwallo”.
A gida Zimbabwe, ba da jimawa ba Chakuzira ya kafa wata cibiyar horas da kwallon kafa, kuma ya yi hayar mai horaswa domin koyar da yara. Har ma ya ce "Kwallon kafa ba wasa ne mai tsada ba. Idan kana sha’awarsa wuri kawai da kwallo kake bukata".
Gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2010 da ta gudana a Afirka ta kudu ta yi matukar tasiri a nahiyar, tare da nishadantar da masu kaunar kwallon kafa. Zimbabwe tana arewa da kasar Afirka ta kudu, kuma ‘yan kasar sun shiga shaukin kallon wannan gasa mai muhimmanci, ko da yake Chakuzira bai samu damar kallon gasar ba. A cewarsa "A wancan lokaci ina shirin rubuta muhimminyar jarrabawar kammala sakandare, yayin da ake ta shagulgulan zuwan gasar ta cin kofin Afirka. Gasa ce dake bayyana kauna, da nishadi da kwallon kafa ke haifarwa. Ina fatan sake ganin wannan gasa nan gaba a rayuwa ta".
A bangaren zaman rayuwa a birnin Beijing kuwa, Chakuzira ya ce rayuwa ce mai dadi kuma mai cike da ayyuka. Kana iya samun komai idan kana da bukata. Akwai tsarin sufuri mai inganci, da na sayayya, da kawancen al’ummun kasashen waje mazauna birnin. Akwai muhalli mai ragewa mutum kewar gida.
Ya zuwa yanzu da Chakuzira ke da shekaru 29 da haihuwa, yana ci gaba da jiran lokacin yanke shawarar komawa gida domin raba ilimin da ya samu a kasar Sin, da kwarewar horas da kwallon kafa daga sassan duniya daban daban.
A cewar Chakuzira, "Zan ci gaba da gina wata gada ta hade yaran Zimbabwe da na kasar Sin. Hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya shafi sassa mabanbanta, ciki har da fannin wasan kwallon kafa da cinikayya. Ina fanan bayar da gudummawar raya wadannan fannoni".