logo

HAUSA

Isra’ila ta kai hari ta sama a tsakiyar Beirut

2024-10-03 15:54:45 CMG Hausa

Tashar talabijin ta Al-Jadeed ta bayar da rahoton cewa, Isra’ila ta kai wani hari ta sama kan cibiyar kiwon lafiya da ke da alaka da kungiyar Hizbullah a yankin al-Bachoura, da ke tsakiyar birnin Beirut a daren jiya Laraba. Rahoton ya nuna bidiyon hayaki mai kauri na tashi daga ginin. Har ila yau harin ta sama ya haifar da barna sosai ga gidaje da ke kusa da kuma ababan hawa. Motocin daukar marasa lafiya da jami'an tsaron farin kaya sun garzaya yankin domin ceto.

Tashar talabijin din ta labarto cewa, jim kadan gabanin harin da aka kai a tsakiyar birnin na Beirut, Isra'ila ta kaddamar da hare-hare masu karfi guda uku a yankin Haret Hreik da ke kudancin birnin Beirut. Kuma rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da kai harin, inda ta bayyana cewa ta kai wani madaidaicin hari a babban birnin kasar Lebanon. (Yahaya)