An samu dauko gawarwakin mutane 25 daga cikin 200 da hadarin jirgin ruwa ya ritsa da su a jihar Niger
2024-10-03 14:38:15 CMG Hausa
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger ta sanar da yammacin jiya Laraba 2 ga wata cewa, ta sami nasarar dauko adadin gawarwakin mutane 25 daga cikin mutane 200 da hadarin jirgin ruwa ya ritsa da su ranar 1 ga wannan wata a yankin Mundi, dake karamar hukumar Mokwa a jihar Niger.
Darakta janaral na hukumar Alhaji Abdullahi Baba Arah ne ya tabbatar da hakan, ya ce daga cikin mutanen da aka samu damar dauko gawarwakin nasu sun hada da mata 4 da maza 21.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Shi dai wannan jirgin ruwa wanda yake dauke da fasinjoji 200 ya taso ne daga garin Mundi zuwa Gbajibo, kuma ya kife kafin ya kai ga inda zai je, nan take dai ma'akatan agaji suka samu nasarar ceto mutane 150.
Daraktan janaral na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Niger ya tabbatar da cewa ma'aikatan hukumar da na ma'aikatar sufuri ta jihar, da kuma kwamatin bayar da taimakon gaggawa na karamar hukumar Mokwa, da kuma sauran 'yan agaji masu zaman kansu, suna aikin hadin gwiwa wajen lalubo ragowar mutanen da suka bace, inda suke aiki har zuwa daren jiya Laraba.
Rahotannin sun bayyana cewa fasinjojin da wannan hatsari ya ritsa da su sun taso ne da nufin zuwa wajen bikin maulidi, ko da yake Malam Habibu Abubakar Wushishi darkatan harkokin yada labarai da tsare tsare na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Niger ya musanta hakan .
“Ba gaskiya ba ne, mu ba mu ji cewa ayarin musulmi ne da za su je maulidi ba, abin da muka sani shi ne an ce jama'a ne wanda suke je cin kasuwa a wani kauye da ake kira Mundi a karamar hukumar Mokwa, kuma bayan sun kammala cin kasuwa za su koma gida wajen karfe takwas da rabi na dare shi ne wannan hadari ya faru, jirgin yana dauke da mutane wanda aka ce sun kai kimanin mutane dari biyu, yanzu kam an kubutar da mutane sun fi 150 wanda suke da rai”
An dai alakanta faruwar wannan al`amari da yin lodin daya wuce kima,sannan kuma da gaza amfani da rigar ruwa daga bangaren fasinjoji.(Garba Abdullahi Bagwai)