Wakilin Sin ya bukaci a kyautata tsarin duniya da gyara rashin adalci da aka yi wa Afirka
2024-10-03 15:12:04 CMG Hausa
A jiya Laraba ne zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Fu Cong, ya yi kira da a kara yin kokari wajen kyautata tsarin mulkin duniya, da kuma gyara rashin adalcin da aka yi wa Afirka a tarihi.
Wakilin ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar a taron kwamitin sulhu na MDD kan hadin gwiwa tsakanin MDD da kungiyar Tarayyar Afirka, Fu ya ce kasashen Afirka sun fita daga mulkin mallaka, sun kuma samu ‘yancin kai na kasa, kuma kasancewarsu mamban MDD ya kawo sauyi da kara fadada tasirinta a duniya. Duk da haka, har yanzu tsarin kasa da kasa yana dauke da rashin adalci da kuma abubuwan da ba su dace ba ga kasashen Afirka, kuma har yanzu suna fama da rashin daidaito na gaskiya wajen samar da tsarin mulki, dama, da kuma madafun iko.
Wakilin ya kara da cewa, a yayin babban taron MDD karo na 79 da aka gudanar a makon jiya, shugabannin kasashen Afirka sun yi kira da a gaggauta yin garambawul ga tsarin mulkin duniya, domin kawar da rashin adalci na tarihi da Afirka ta yi fama da shi na tsawon lokaci. Kuma kasar Sin na goyon bayan bukatun Afirka kan adalci. (Yahaya)