Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kan Isra’ila
2024-10-02 16:05:35 CMG Hausa
Iran ta yi ruwan makamai masu linzami kusan 180 kan Isra’ila a yammacin ranar Talata sakamakon farmakin da sojojin Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Lebanon wanda ya kashe shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah.
Tarin makamai masu linzami sun sauka kan Isra'ila da misalin karfe 19:30 agogon kasar, lamarin da ya haifar da tashin alamar gargagi yayin da mazauna yankin suka nemi mafaka. An ji karar fashewar makaman a birnin Kudus yayin da na'urorin tsaron sararin samaniyar Isra'ila suka yi nasarar kabe wasu makamai masu linzami na Iran, kamar yadda wakilan kamfanin dillancin labarai na Xinhua suka shaida.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin cewa, Isra'ila za ta mayar da martani kan harin makami mai linzami da Iran ta kai. Inda ya ce, "Duk wanda ya kai mana hari, za mu kai masa hari." Netanyahu ya fadawa taron majalisar ministocin tsaro da ya mayar da hankali kan yiwuwar kai hare-hare da kuma kutsewar sojojin kasa cikin Lebanon.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a dandalin sada zumunta na X bayan harin, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da "fadada rikicin yankin Gabas ta Tsakiya, ta hanyar kai hari bayan hari." Ya ce dole ne a daina hakan kuma a tsagaita bude wuta nan da nan. (Yahaya)