logo

HAUSA

Taya kasashen Sin da Najeriya murnar zagayowar ranar kafa sabuwar kasa da ranar samun ’yancin kai

2024-10-02 07:29:26 CGTN Hausa

Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce mai muhimmanci ga jamhuriyar jama'ar kasar Sin da tarayyar Najeriya, rana ce da aka kebe domin al'ummomin kasashen biyu su gudanar da murnar bikin ranar kafa kasa da ranar samun 'yancin kai na kasashen biyu bi da bi, yayin da kasar Sin ke cika shekaru 75 da kafuwa ita Najeriya kuma ke cika shekaru 64 da samun ’yancin kai.  

A cikin shekaru 75 kacal, kasar Sin ta tashi daga kasa mai fama da talauci, da rashin ci gaba, zuwa babbar kasuwar tattalin arziki ta duniya, kuma babban jigo a harkokin mulkin duniya. Kasar Sin na daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya. Najeriya a nata bangare kuwa, tana ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannoni daban daban a nahiyar Afirka. Yayin da muke taya wadannan kasashe biyu murnar wannan muhimmiyar rana a shirinmu na yau, za mu duba irin ci gaba da kasashen biyu suka samu kawo yanzu, da kuma nasarorin da suka samu a hadin gwiwar dake tsakaninsu cikin shekaru 50 da suka gabata. 

A cikin shekaru 75 da suka gabata, GDPn kasar Sin ya tashi daga yuan biliyan 67.9 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 9.67 a shekarar 1952 zuwa yuan triliyan 126 a shekarar 2023, wanda ya kai kusan kashi 17 na tattalin arzikin duniya. Hakan na nufin  karuwar darajar tattalin arzikin kasar sau 223, kuma GDP na kowane mutum ya karu daga yuan 119 a shekarar 1952 zuwa sama da yuan 89,000 a bara. A cikin wadannan shekaru Har ila yau, kasancewar Najeriya kasa mafi yawan al'umma a Afirka, ta tabbatar da tasirinta a nahiyar ta hanyar jagorantar yakin neman 'yantar da kasashen Afirka daga mulkin mallaka, kuma a wasu lokuta, ta taimaka wajen maido da mulkin demokradiyya da dai sauran muhimman gudummawa da take bai wa kasashen Afirka.

Da'irar abokantaka ta kasar Sin ta kara habaka, inda aka kulla huldar diflomasiya da jimillar kasashe 183 ya zuwa watan Satumba, lamarin da ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiyar duniya. Kazalika a watan Satumba, shugabannin kasashen Sin da Afirka sun yi nasarar gudanar da taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na shekarar 2024 a nan birnin Beijing, inda aka tsara shirye-shiryen inganta hadin gwiwar Sin da Afirka a sabon zamani.  

A cikin shekaru 75 da suka gabata tun bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, musamman tun bayan da aka fara yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a shekarar 1978, kasar Sin ta himmantu wajen bin hanya ta musamman ta bude kofa ga kasashen waje, wadda ke nuna halaye na musamman na kasar Sin. Ta hanyar yin hadin gwiwa da yin gasa a fannin tattalin arziki na kasa da kasa, kasar Sin tayi sauyawa mai ban mamaki ta zama tattalin arzikin da ya rungumi bude kofa ga kasashen waje. Wannan sauyin ya zurfafa hadin gwiwar cinikayya da kasashen ketare tare da habaka da kuma kara saukaka ka'idojin bude kofa. Rungumar wadannan yanayin yana da mahimmanci ga ci gaban kasa da hadin kai na duniya. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)