logo

HAUSA

Kudin bincike da gwajin kimiyya na Sin ya karu da 8.4% a shekarar 2023

2024-10-02 20:20:48 CMG Hausa

Wakilinmu ya samu labari daga hukumar kididdiga ta kasar Sin yau Laraba cewa, kudin da aka kashe kan bincike da gwajin kimiyya na Sin wato R&D, ya ci gaba da bunkasa, kuma karfin zuba jari na ci gaba da karuwa.

A shekarar 2023, Sin ta zuba jarin yuan triliyan 3.33571 kan ci gaban bincike da gwajin kimiyya, wanda ya karu da kashi 8.4 bisa dari a kan shekarar 2022. A shekarar 2023, adadin kudaden gudanar da bincike kan ilmomin tushe na kasar ya kai yuan biliyan 225.91, wanda ya karu da kashi 11.6 bisa dari a kan shekarar 2022.

Idan aka yi la'akari da yankuna, akwai larduna da birane bakwai da karfin zuba jarinsu a fannin ya zarce matsakaicin karfi na dukkan sassan kasar, wato Beijing, Shanghai, Tianjin, Guangdong, Jiangsu, Zhejiang da kuma Anhui.(Safiyah Ma)