Najeriya ta fara shirye-shiryen debe 'yan kasar ta dake zaune a Labanon
2024-10-02 14:44:59 CMG Hausa
Fadar shugaban Najeriya ta sanar da shirin ta na fara debe `yan Najeriya da suke zaune a kasar Labanon, bayan harin baya-bayan nan da kasar Iran ta kai Isra'ila.
Mashawarcin shugaban na tarayyar Najeriya a kan sha'anin kafofin sada zumunta Mr. Dada Olusegun ne ya tabbatar da hakan jiya talata 1 ga wata a Abuja .
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.、
Kamar dai yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da ya tura ta shafi sa na X, mashawarcin shugaban na Najeriya ya bukaci duk wani dan Najeriya da yake zaune a kasar ta Labanon da ya je ofishin jakadanci Najeriya dake kasar da cikakkun takardun sa domin dauko shi zuwa gida.
Sanarwar ta ce akwai yiwuwar rikicin yankin zai kara yin kamari tun bayan da kasar Iran ta harba makamai masu lizami cikin kasar Isra'ila wanda tabbas akwai yiwuwar mayar da martani daga Isra'ila.
Ko da a cikin jawabin da ya gabatarwa al'ummar kasar ranar 1 ga wata shugaban na tarayyar Najeriya ya umarci duk wasu 'yan Najeriya da suke zaune a yankin na Labanon da su shirya domin debo su zuwa gida, domin tabbatar da kare rayukan su. (Garba Abdullahi Bagwai)