logo

HAUSA

Sin ta bukaci NATO da ta gyara mummunan tunaninta game da kasar Sin

2024-10-02 19:47:40 CMG Hausa

A ranar 2 ga watan Oktoba, tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar Turai ta amsa tambayoyin manema labarai game da furucin da kungiyar tsaro ta NATO ta yi a baya cewa, kasar Sin ta kasance babbar mai goyon bayan yakin Rasha kan Ukraine, don haka NATO na bukatar karfafa dangantaka da kasashen “Indo-Pasifik”

Mai magana da yawun tawagar kasar Sin a kungiyar tarayyar Turai ya bayyana cewa, kasar Sin ta lura da furucin da NATO ta yi. Matsayin kasar Sin game da rikicin Ukraine a bayyane yake, kuma a ko da yaushe tana maida hankali kan samar da hanyoyin warware rikicin ta hanyar siyasa, da samar da zaman lafiya da tattaunawa. Ba da dadewa ba, kasar Sin da sauran kasashe "masu tasowa na duniya" irin su Brazil suka kafa kungiyar "abokan zaman lafiya" kan rikicin Ukraine a MDD, domin sa kaimi ga samar da yanayi na tsagaita bude wuta, da kuma maido da shawarwarin zaman lafiya. Kasashen duniya sun amince da matsayin kasar Sin na gaskiya da adalci da kuma rawar da take takawa. Kana kasar Sin ta jaddada cewa, game da batun rikicin Ukraine, yin watsi da daukar alhaki, da kafa karamar kungiya ba za su taimaka wajen warware rikicin ba. Kasar Sin ta bukaci kungiyar NATO da ta yi watsi da tunanin yakin cacar baka, ta kuma gyara mummunan tunaninta a kan kasar Sin, da daina tsoma baki a harkokin Asiya da Pasifik, da kara yin wasu abubuwa da za su taimaka wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, maimakon akasin haka. (Yahaya)