logo

HAUSA

Cikin shekara guda sauye-sauyen tattalin arziki ya sanya Najeriya samun dala buliyan 30 daga masu saka jari 'yan kasashen waje

2024-10-02 14:47:17 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar ya samu karuwar dala buliyan 30 a cikin shekara guda daga masu saka jari 'yan kasashen waje sakamakon garanbawul din da gwamnatin sa ke yi wa tattalin arzikin kasar.

Ya tabbatar da hakan ne cikin jawabin da ya gabatarwa al'ummar kasar jiya talata 1 ga wata, a cigaba da shagulgulan bikin cikar kasar shekaru 64 da samun 'yancin kai.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kamar yadda shugaban ya fada, sauye sauye daban daban a manufofin gwamnati ta fuskar tattalin arziki, ya yi sanadin samun karin kudaden da kasar ke samu daga 'yan kasuwa masu zuba jari 'yan kasashen waje zuwa dala buliyan 30 a tsakanin shekara guda kacal.

Ya ce ya zama wajibi a yi kwaskwarima ga harkokin tattalin arzikin kasa wanda yake tangal-tangal, inda ya ce muddin dai ba a dauki wani mataki na gaggawa ba, to kuwa za a tsinci kai cikin wani yanayi na rashin tabbas a fatan da ake yi na samun kyakkyawar makoma.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen karfafa tsarin kasuwanci ba tare da wata takura ba, tare da sassauta dokokin shiga da fita na 'yan kasuwa masu sha'awar zuba jari a Najeriya, yayin da kuma ana cigaba da gudanar da tsare tsare masu karfi da za su bunkasa sha'anin zuba jari a bangaren hakar danyen mai dake kan tudu.(Garba Abdullahi Bagwai)