logo

HAUSA

Sin ta kai kara kan karin haraji kashi 100% da Canada ta sanya kan EV da aka shigo da su daga Sin

2024-10-02 16:27:54 CMG Hausa

Yau Laraba, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayoyin 'yan jarida kan aiwatar da karin harajin kwastam kan motocin dake aiki da lantarki ko EV na kasar Sin da Canada ta yi, da kuma fitar da jerin sunayen karshe na kayayyakin karafa da gorar ruwa na kasar Sin da za su kara haraji.

Bisa sanarwar da Canada ta yi a baya, karin harajin 100% da ta sanya kan motocin lantarki da aka shigo da su daga Sin zai fara aiki a hukumance a ranar 1 ga watan Oktoba. Bugu da kari, Canada ta kuma sanar da jerin sunayen kayayyaki na karshe wanda ya hada kayayyakin karafa da gorar ruwa na kasar Sin da za su sanya wa karin harajin kashi 25 cikin dari daga ranar 22 ga watan Oktoba.

A nata martanin, ma'aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana cewa, matakin da Canada ta dauka ya saba wa ka'idojin tattalin arziki na kasuwa, da yin gasa ta gaskiya, wanda ya kawo illa ga hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na yau da kullum a tsakanin kamfanonin kasashen Sin da Canada, ya kuma yi matukar mummunan tasiri ga huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, tare da kawo cikas tare da gurgunta tsarin masana’antun duniya da tsarin samar da kayayyaki. Sin tana adawa da hakan kwarai da gaske.

Kasar Sin ta riga ta shigar da kara a kungiyar WTO kan yadda kasar Canada ke nuna ra'ayin bangaranci da ba da kariyar cinikayya, kuma ta kaddamar da bincike kan matakan da Canada ta dauka bisa doka. (Safiyah Ma)