Ana sa ran tsarin layin dogo na kasar Sin zai yi jigilar fasinjoji miliyan 21 a yau Talata
2024-10-01 16:13:21 CMG Hausa
Yau Talata, 1 ga wata ne rana ta farko ta lokacin hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, inda tsarin layin dogo na kasar yake samun kololuwar kwararar fasinjoji. Kafar CMG ta ruwaito labari daga kamfanin kula da jiragen kasa na kasar Sin na cewa, a yau, ana sa ran jigilar fasinjoji miliyan 21, inda jirage 12,737 za su yi zirga-zirga, ciki har da karin jiragen kasa 1,476.
A ranar 30 ga watan Satumba, tsarin layin dogo na kasar Sin ya dauki fasinjoji miliyan 17.283, ciki har da fasinjoji miliyan 1.416 da suka bi ta tashoshin birnin Beijing, yayin da miliyan 3.437 suka bi ta tashoshin birnin Shanghai.(Safiyah Ma)